BARR.JALLO YA HALACCI BIKIN KADDAMAR DA GININ UBEC MODEL SMART SCHOOL HADEJIA DA KUMA KADDARAMAR DA RABON #EDUKEKKE 19/01/2022..





Mai Girma Dan Majilissar Jiha Mai Wakiltar Karamar Hukumar Hadejia Kuma Shugaban Kwamatin Shari’ah Na Majilissar Dokokin Jihar Jigawa Mallam Abubakar Jallo tare da dandazon jama,arsa sun Halacci taruka guda biyu yau a cikin garin Hadejia.
Mai girma Dan majalissar ya Halacci Taron aza harsashin Ginin sabuwar makarantar hukumar ilimi ta baidaya ( UBEC MODEL SMART SCHOOL HADEJIA.
Sannan Dan majalissar ya Kara Halattar Bikin Kaddamar Da Rabon Kekuna Da Mashina Wanda Mai Girma Sanatan Jigawa Ta Gabas Distinguish Senator Ibrahim Hadejia Ya Gudanar.
Mai Girma ‘Dan Majilissar ya nuna Farin Cikinsa, Kuma Yayi Addu’ar yadda aka fara Ginin wannan makaranta lafiya Allah yasa a gama lafiya Kuma Allah yasa albarka a cikin wannan makaranta. Sannan ya Kara yin addu,a Duk Wanda Allah Yasa Da Rabonsa A Wannan Kaya Allah yasa lafiya ta mora.
Thank you Jagoran Al,ummar Hadejia.

Leave a comment