Cikeken Rohto akan Rasuwar Yarinyar da aka Yi kidnapped, Hanifa Abubakar #hanifa_death😭😭

Ashe duk neman da akeyi wa HANIFA, Malamin Makarantarsu ne ya saceta ya bukaci a biya fansar miliyan shida(6,000,000).

Da yaga ta ganeshi sai ya kasheta ya bunne ta a rami a cikin makarantar.

Allah ka kiyashe mu sharrin zamani.

Allah ya cigaba da tonawa masu irin wannan hali asirinsu.
ƘARIN BAYANI: Waɗanda su kai garkuwa da Hanifah a Kano sun kashe ta duk da an biya su kuɗin fansa

Waɗanda su ka yi garkuwa da Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5 a Jihar Kano, sun kashe ta duk da sun karɓi wani abu da ga cikin naira miliyan 6 da su ka nemi a basu a matsayin kuɗin fansa.

Baffan ta, Suraj Suleman ne ya tabbatar da kisan nata da kuma gano sassan jikin ta a wata tsohuwar makarantar kudi a unguwar Tudunwada a Kano.

A cewar sa, da farko, wanda yai garkuwa da Hanifah, ya kai wajen matar sa, amma sai ta ƙi ta karɓe ta.

“Da ga nan ne sai ya kaita Tudunwada inda ya ke da wata makarantar kuÉ—i. Sai ya haÉ—a mata shayi da shinkafar É“era a ciki ta sha.

“Bayan ta sha shayin, sai ta mutu. Da ga nan sai wanda yai garkuwar da ita ya daddatsa jikin ta ya binne ta a cikin makarantar,” in ji baffan nata.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an kama wadanda su ka yi garkuwa da Hanifah ne a wajen titin Zariya a jiya daddare lokacin da su ke ƙoƙarin karɓar cikin kuɗin fansar.

A tuna cewa tun a ranar 4 ga watan Disambar 2021 ne masu garkuwa da mutane su ka É—auke Hanifah bayan da su ka zo a adaidaita-sahu su ka yaudare ta su ka sungume ta

Wa yan nan  sune iyayin #Hanifa da aka kashi.
A dauka ciwa kazo musu ta,aziya ne

Mezakuce musu,

Allah ya mata rahama🤲 😭

Pages: 1 2

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started