Zamfara: ‘Kyale kowa ya mallaki makami na da haɗari’

Sa’o’i 5 da suka wuce

Masana a harkar tsaro sun bayyana cewa matakin da gwamnatin jihar Zamfara da ke Najeriya ta dauka na kyale farar-hula su mallaki bindiga yana da matukar hadari.

A karshen makon jiya ne gwamnatin ta sanar da wannan mataki tana mai cewa ta dauke shi ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji.

Sai dai wani masani kan harkar tsaro a yammacin nahiyar Afirka, Audu Bulama Bukarti, ya ce shawarar da gwamnatin Zamfara ta yanke za ta iya kawo kazancewar rikici tsakanin Hausawa – mazauna cikin garuruwa da Fulanin daji – wadanda ke zargin ana masu rashin adalci.

Ya ce: “Yanzu haka Fulani na koke-koken cewa ‘yan banga na Hausawa sukan je rugage ne su kashe duk Bafulatanin da suka gani, su kona dukiyarsa saboda suna ganin duk Bafulatani yana cikin ‘yan bindiga.”

“Haka kuma Hausawa mazauna cikin gari suna zargin cewa ana kashe su da garkuwa da su ne saboda kabilanci da Fulani suke nuna masu,” a cewarsa.

Ya kara da cewa idan aka ce kowa ya dauki bindiga to kuwa duk Bafulatanin da Hausawa suka gani a daji kashe shi za su yi, haka nan ma duk Bahaushen da Fulani suka gani su ma kashe shi za su yi.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started