



-A Cikin Ƙasa Da Kwanaki Uku Da Ya Raba Tallafin Jari Naira Dubu Ashirin-Ashirin Ga Mutane 5,000 Maza Da Mata Masu Ƙananan Sana’o’i A Birnin Jos, Kaftin Ahmad Musa A Jiya Ya Sake Gwangwajewa Wani Bawan Allah Da Kyautar Gida A Jihar Kano.
Yau Talata, 28 ga watan June, 2022.
Fitaccen ɗan ƙwallon ƙafan Nageriya na ƙungiyar Super Eagle Kaftin Ahmad Musa ya tallafawa wani bawan Allah mabuƙaci da kyautar katafaren gida a yankin mai suna Ado da ke mazaɓar Sallare Babban Giji kusa da makarantar Islamiyya ta Tahfizul islamiya School a Jihar Kano.
Ko da a ƴan kwanaki biyu baya, Captain Ahmad Musa ya yi rabon tallafin jarin dogaro da kai ga masu ƙananan sana’o’i mutum 5,000, maza da mata inda kowane mutum ɗaya ya samu Naira 20,000 domin ya bunƙasa sana’arsa. Captain Ahmad Musa mutum ne wanda ya yi shuhura wajen tallafa jama’a masu ƙaramin ƙarfi a sassa daban-daban na Nageriya.

Leave a comment