
Kwana biyu bayan dawowarsa daga taron koli na shugabannin kungiyar Commonwealth a Kigali babban birnin Rwanda, Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tashi a yau Talata zuwa Portugal a ziyarar kwana hudu.
A wata sanarwa da kakakinsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ya ce shugaban zai gana da takwaransa na Portugal, Shugaba Marcelo Rebelo, sannan kuma za a karrama shi da lambar girmamawa da kuma ta Masarautar kasar a ziyarar.
Ana sa rana shugabannin biyu za su jagoranci wani babban taron tattaunawa da kulla yarjeniyoyi na kasashen biyu, sannan kuma su sanyo hannu a kan abubuwan da suka amince a tsakaninsu.
Shugaban na Najeriya zai kuma ziyarci majalisar dokokin kasar ta Portugal inda zai tattauna da shugabanta Dakta Augusto Santo Silva, da kuma Firaministan Portugal din, Antonio Costa
Shugaba Buharin zai kuma gabatar da jawabi ga gamayyar ‘yan kasuwa na Najeriya da Portugal, kana daga bisani ya yi tattaunawa ta musamman da wasu zababbun ‘yan kasuwar na Portugal masu zuba jari.
Haka kuma shugaban na Najeriya zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a kan tekunan duniya, taron da aka fara ranar jiya Litinin a Lisbon, wanda kuma za a kammala ranar 1 ga watan Yuli
Masu raka shugaban sun hada da Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed da Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Adeniyi Adebayo.
Sauran sun hada da Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzkin Harkokin Intanet, Isa Pantami, na daga cikin masu rufa wa shugaban baya.
A tawagar Buharin akwai kuma sauran mukarraban gwamnatinsa kan tsaro da sauransu.
Za su koma Abuja a ranar Asabar 2 ga watan Yuli, kamar yadda sanarwar ta ce.

Leave a comment