
Babban kamfanin samar da makamashi na Afirka ta Kudu ya sanar da cewa akwai yuwuwar kara katse wutar lantarki a kasar muddin ba a kawo karshen yajin aikin da ma’aikatansa ke yi ba a yanzu.
A yayin wani taron manema labarai na gaggawa shugaban kamfanin wutar, Eskom, Andre Ruyter, ya ce, matsalar za ta kai ga ana katse lantarki har tsawon sa’a shida a rana.
Ma’aikatan na bukatar a kara musu albashi da kashi 10 cikin dari, wanda hakan ya zarta abin da kamfanin, wanda ya dogara ga tallafin gwamnati wajen ceto shi, ya ce zai iya ba su.
Sama da mako daya da ya gabata ne ma’aikatan suka fara tafiya yajin aiki, abin da ya jefa kasar cikin matsalar rashin wuta a tsakiyar huturu.
Daman tsawon shekaru babban kamfanin samar da lantarkin na Afirka ta Kudu ke fama wajen samar da wuta saboda ya dade cikin hali na rashin samar da wadatattun kayayyaki da kudaden tafiyarwa.
Tuni aka fara ganin illar matsalar rashin wutar a kan tattalin arzikin kasar da kuma rayuwar jama’a musamman talakawa.

Leave a comment