Man fetur ɗin Sri Lanka na dab da ƙarewa

Gwamnatin Sri Lanka ta ce watakila ba za ta iya shiga da man fetur cikin ƙasar nan da makonni uku ba, abin da zai zama wani sabon ci baya ga tattalin arzikin kasar.

Man da kasar ke da shi dai ya kusan ƙarewa kuma ana dauninsa ne inda ake ba da fifiko ga motocin asibiti da na sufuri da kuma masu jigilar kai abinci.

Yanzu haka dai an rufe makarantu kuma an buƙaci mutane da su yi aiki daga gida. Lamarin wanda ya fara daga bashi yanzu ya jefa al’ummar Sri Lanka cikin wani halin tagayyara inda miliyoyi ke goggoriyon samun abinci ma.

Rugujewar tattalin arzikin kasar ya kuma haddasa wani rikicin siyasa da ya kai ana ta hura wa Shugaban Gotabaya Rajapaska wutar ya sauka.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started