Sarkin Katsina ya ba Saddik Musa Kaita Sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta

Sarkin Katsina Dakta Abdulmuninu Kabir Usman ya tabbatar wa Saddiq Musa Kaita da Sarautar Sarkin Dawaki Mai Tuta.

A cikin wata takarda da sarkin ya saka wa hannu, sarkin ya ce ya tabbatar masa da ba shi wannan sarauta kuma zai saka ranar da za a yi naɗi.

A kwanakin baya ne dai sarkin ya bai wa Saddik Sardaunan Katsina, sai dai bayan kwana guda da bayar da sarautar aka dakatar da bayar da sarautar bisa wasu dalilai.

Saddik jika ne ta ɓangaren uba ga sarkin Fadan Katsina Isma’ila Damale wanda shi kuma ɗa ne ga Wazirin Katsina na farko Haruna Kaita.

Haka kuma ta ɓangaren uwa jika ne ga Makaman Katsina Marigayi Tukur Idris Nadabo hakimin Bakori.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started