INNALILLAHI WA INNA’ILAIHIRRAJU’UN
Allah Mun Tuba, Allah Ubangiji Ya Kawo Mana Dauki




Al’ummar Masarautar Hadejia na bukatar taimako, bisa halin da muka tsinci kan mu na iftila’in Ruwa (Flood) wanda ya jawo sanadiyyar rasa rayuka, dukiyoyin Al’umma, Gonaki, gidaje, rumfunan kasuwa da sauran su
Jama’a na cikin wani hali matsanan ci da tausayi da kuma bukatar taimakon bayan Allah wanda Allah ya hore musu.
Wannan Hotuna da kuke gani wasu sassa ne na Ambaliyar Ruwa a yankin Masarautar
Cikin hotunan akwai Hanyar Gamayin wacca ruwa ya cika ta wacca abin hawa baya iya wucewa sai an hau ta kwalekwale wanda ko jiya saida wani ya kife wanda yayi sanadiyar rasuwar mutane.
Akwai garin Kubayo dake karamar hukumar Kirikasamma wanda halin da ake ciki da yammanan ruwa ne ke shiga cikin garin wanda alummarmar gari duka sune ɗebe kayansu suna barin garin.
Ciki akwai garin Yamidi dake karamar hukumar Auyo wanda suma suke cikin barazanar ruwa inda yaci wani yankin.
Da gadar kogin Hadejia wacca kogin shima ya cika sosai inda yaci gonakin ya tsallaka har zuwa titin Baturiya inda yake tsallaka wa daya gefen inda yake haduwa da kogin Dole yake shiga garuruwa da gonaki.
Tuni gari irin na Maragwado da Gilakoci dake karamar hukumar Kirikasamma ruwa ya zagaye su, inda yake tilasta wa al’ummar garin tashi suwa sai ta kwalekwale, wasu kuma suna cikin garuruwan wanda baza su iya fitowa ba sai da kwale-kwale.
Allah kawowa alummarmu sauƙin wannan iftila’in, wanda suka rasu Allah jikansu Allah karbi shahadarsu, wanda suka rasa muhalli da amfanin gona Allah mayar musu da Alkairi

Leave a comment