
Yau za’a fara (ko aka fara) System Upgrade akan Satoshi App:
Core DAO Team sun sanar cewa yau 19 ga December za suyi aikin sauya fasalin Application din da aka yi Mining din Core akan sa, sunce aikin zai fara ne dai dai 19 ga December, sai dai basu saka time directly ba, a gaban Date din sai suka ce 19 UTC, hakan yana nuna ‘karfe 1:00am na daren da muka wuce (Agogon Nigeria).
Idan Kuma suna nufin ranar 19 ga watan December, a dai dai ‘karfe 19 na UTC, toh idan muka buga lissafi zai kama ‘karfe 4:00pm na yammacin yau Litinin Agogon Nigeria.
Amma nafi fahimtar ‘karfe 1 na daren da muka wuce ne, saboda me?
Saboda a cikin sanarwar sunyi amfani da kalmar “intermittently”.
Abunda kalmar take nunawa shine aikin ne da za’a yi amma ba za’a dauke kafa gaba daya ba, wato ba Full ko Complete shutdown za suyi ba, kalmar tana nuna wani lokaci zaka iya hawa kaga Application din Yaki budewa, ko kuma ka hau kaga babu Coins din ka, wannan ba matsala bace a wannan tsakanin, wato daga Litinin zuwa Talata.
Sanarwar tace aikin zai dauke su tsawon kwana daya, wato daga 1 na daren jiya, zuwa 1 na daren yau da zamu shiga (in sha Allah).
Dan haka idan kaga wata matsala kada ka damu, zuwa daren da zamu shiga zata warware in sha Allah.
Kuma daga goben kowa zai sake Updating Application din, domin shiga Next Level.
As they previously announced, Satoshi Application ba mallakar Core DAO ne gaba daya ba, Partnership ne da kamfanoni daban daban, saboda haka abun dole zai zo da haka, kuma yana nuna akwai jiga jigan mutane da kamfanoni da ‘yan gani kashenin Satoshi Nakamoto a cikin Core.
Allah yasa mu dace…..

Leave a comment