MARA ZASU DAUKI P2P MERCHANT MUTANE 1,000.

P2P MERCHANT: Shine wanda Mara zasu dinga bama dala a farashi mai sauki yana siyarwa mutane ta hanyar amfani da MARA WALLET, Ana samun makuddan kudade amma akwai dokoki da sharadi da suka saka dangane da zama p2p merchant din.

Dokokin sune….

1. Dole sai ya zamana kana da wallet din MARA

2. Ana buqatar iya wanda zai iya saka kudi ne, ya nemi kudi. Dole aikin Marchant yana buqatar jari.

3. Dole wanda zai zama Marchant din zai dinga kasuwancin P2P din nasa ne a MARA.

4. Ana buqatar wanda yake da sani akan harkar crypto.

Bayannan da ake buqata sune:

1. Sunanka da ka bude Wallet din Mara

2. Email da kayi amfani da ita gurin budewar

3. Numbar wayarka da kayi amfani da ita gurin bude wallet.

4. Sunan garin da kake, da local government

5. Full address naka Misali (Kofar gidan sarki layin galadima, gwale local government kano state Nigeria.

6. Investing Capital (Shine adadin kudin da zaka iya sakawa a kasuwancin P2P din). Wannan yana da bala’in mahimmancin gaske.

7. Monthly Trading Volume (Adadin trading din da zakayi a wata guda). Misali zaka saka $500 sannan kullum zaka dinga trading da ita sau biyu, kaga kenan kullum zaka dinga trading na $1000, a cikin wata daya zakayi trading na sau talatin kaga kenan Monthly Trading Volume dinka zai kama $30,000)

Duk wanda yake ra’ayi zuwa 6 na yamma zasu bayar da form da duk wanda ya cike wannan ka’ida kuma yake ra’ayin aikin zai iya cikewa.

NOTE: Idan baka cike ka’ida daya ba kada ka cike wannan form din.

Allah yasa mu dace🙏 

One response to “MARA ZASU DAUKI P2P MERCHANT MUTANE 1,000.”

Leave a reply to Abdul KimeeyaTv Cancel reply

Design a site like this with WordPress.com
Get started