
Sa’o’i 3 da suka wuce
Hukumar kula da sufurin mota a jihar Kano (KAROTA) ta ce tana ci gaba da neman wani mai baburin a-daidaita-sahu ruwa a jallo bayan ya ɗauko wata kura da ta yi ƙoƙarin tserewa a tsakiyar kasuwa.
Hukumar ta ce jami’anta suna neman mai a-daidaita-sahun saboda abin da ya yi ya saɓa wa doka, don kuwa bai kamata ya ɗauko dabbar daji a cikin babur ba.
Mai magana da yawun hukumar, Nabulisi Abubakar ya shaida wa BBC cewa kura ba tunkiya ko akuya ba ce, dabba ce mai hatsari da bai kamata a bar ta tana gararamba a cikin mutane ba.
“Muna ci gaba da neman ɗan a-daidaita-sahun a yanzu haka, kuma muna da lambobin babura guda biyu da muke zargi, matuƙar kuma muka kama direban, to kotu za mu kai shi kai tsaye.

Leave a comment